Atiku ya musanta zargin yi wa INEC zanga-zanga

0

Wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya musanta zargin cewa ya na shirya gagarimar zanga-zanga a kan sakamakon zaben shugaban kasa na 2019.

Abubakar wanda shi ne dan takarar jam’iyyar PDP, ya kalubalanci sakamakon zaben, inda har ikiraari ya yi cewa shi ne ya lashe zabe ba Shugaba Muhammadu Buhari na APC ba.

Sannan kuma ya ce ya na da sakamakon zabe sahihi da suka zakulo daga rumbun ajiyar sakamakon zabe na INEC a kwamfuta, wato ‘server’, wanda ya nuna Atiku ne ya yi nasara ba Buhari ba.

Sai dai kuma ita INEC ta karyata wannan zargi, ta ce ba ta da wani rumbun da take tattara bayanai a intanet, wato ‘Server.’

Kakakin Yada Labarai na Atiku Abubakar, Paul Ibe, ya furta a yau Lahadi cewa rahoton da ake yadawa, wai Atiku na shirya gagarimar zanga-zanga, ba gaskiya ba ce, duk karya ce.

Ya ce wadanda ke yada wannan kazafi duk masu yi wa Atiku Abubakar hassada ne da kuma masu neman bata masa suna da kima da mutunci.

“Ina so kowa ya sani cewa Atiku Abubakar ya yarda da bin doka, kuma ya aminta da kiyaye dokokin Gwamnatin Tarayyyar Najeriya. A shekaru 40 da ya shafe ya na siyasa, bai taba yin wani furucin da ya ci mutunci ko amanar dimokradiyya ba, don haka ba zai yi ba, kuma ba zai fara a yanzu ba.

Ya ce ya bar dukkan masu yi masa batanci da kazafi da kirkirar karya ga Allah.

Share.

game da Author