Hukumar Kididdigar Alkalumma ta Kasa, wato NBS, ta bayyana yadda harkokin hada-hadar sha, saye da sayar da giya ke bunkasa a Najeriya.
Rahoton baya-bayan nan da NBS ya fitar, ya nuna cewa a shekarar 2016, an sha barasa ta kimanin naira bilyan 208 a Najeriya.
Wannan adadi kamar yadda hukumar NBS ta nuna, ya ma zarce kasafin kudin da Jihar Ondo ta kashe gaba daya a wancan shekara.
Jihohin Kudu Maso Kudu ne aka fi kwankwadar barasa, inda a shekarar 2016 suka sha ta naira biliyan 74.4. wadannan jihohi sun hada da: Delta, Edo, Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom da Cross Rivers.
Shiyyar Arewa Maso Yamma ce ba a sha barasa da yawa kamar yadda aka bugu a 2016 ba. Domin alkaluman kididdigar NBS ya nuna cewa a jihohin Kaduna, Katsina, Kebbi, Kano, Sokoto da Zamfara an sha ta naira biliyan 2.6 kacal.
An sha barasa an bugu a Shiyyar Kudu Maso Gabas, har ta naira bilyan 44a jihohin Imo, Anambra, Abia, Ebonyi, Enugu da Ebonyi.
Shiyyar Arewa ta Tsakiya ce aka kwankwadi barasar naira bilyan 30, sai kuma Kudu maso Yamma suka yi mankas da barasar naira bilyan 37.
Shiyyar Arewa maso Gabas sun bugu da barasar naira biliyan 19.6
Sai dai kuma bain mamaki, kididdigar ta nuna cewa mazauna karkara ne suka fi shan giya, inda cikin 2016 suka sha ta naira bilyan 125. Yayin da mazauna birane suka sha ta naira bilyan 82.5.
Amma kuma wani jami’in Hukumar Kare Lafiyar Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), mai suna Abubakar Jimoh, ya bayyana damuwa da yadda ake samun giya barkatai a cikin kasar nan, musamman ma a cikin ‘yar leda.
Ya ce wannan barasa da ake sayarwa cikin ‘sacet’, ta yawaita ko’ina, ta yadda jama’a ke samun damar shan barasa a duk lokutan da suka ga dama.
Daga nan sai ya ce za su fito da ka’idoji domin takaita samun giya barkatai a cikin al’umma.
A na ta bangaren, Hukumar Binciken Cutar Daji ta Kasa, ta ce barasa na daya daga cikin abinda ke haddasa cutar kansa a kasar nan.
“Kashi 1 bisa 10 na cutar kan sa duk giya ce ke haddasa shi. sannan kuma kashi 4.7 na wadanda suka kamu da cutar kansa a cikin shekarar da ta gabata, duk shan barasa ne ya haddasa musu.”