Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa yawan jam’iyyu har 91 da aka yi wa rajista kuma suka shiga zabe, ya kawo mata cikas da kuma haifar da matsaloli wajen gudanar da ayyukan hukumar.
Kwamishinan Zabe mai Kula da Jihohin Kwara, Kogi da Nasarawa, Mohammed Haruna ne ya bayyana haka a wurin wani taro a Kwara a kan tattauna yadda aka gudanar da zabukan 2019.
Da ya ke tattaunawa da manema labarai, ya ce akwai kararraki har 700 daga sassa daban-daban na kasar nan.
Sai dai kuma ya ce har yau babu wani kalubalantar zabe daga jihar Jigawa. Amma kuma daga jihar Imo an shiga da karar rashin aminicewa da sakamakon zabe har sau 77.
Sannan kuma ya ce akwai wasu kararrakin har sama da 800 tun na kalubalantar sakamakon zabukan fidda-gwanin da jam’iyyu suka gudanar a kasar nan.
“Don haka idan ku ka dubi irin wannan matsaloli da muke fuskanta, za ku fahimci cewa akwai matukar bukatar a sake duba yawan wadannan jam’iyyun siyasa.
“Lallai akwai bukatar duba yawan wadannan jam’iyyu, domin jama’a su kan su sun fara kukan cewa jam’iyyu 93 sun yi matukar yawa.” Inji Haruna.
Haruna ya kara da cewa yawan jam’iyyu har 73 da suka shiga zaben shugaban kasa shi ne babbar matsalar da ta fara afka wa hukumar zabe, INEC.
“Ba mu yi tsammanin za mu fuskanci matsala sosai wajen buga takardu kuri’un jefa kuri’a ba, musamman wajen tsawo ko fadin takardar jefa kuri’a ko wadda ake tattara sakamakon zabe.
“Yayin da wadannan kayan zabe suka fara iso mana, sai muka gane cewa lallai akwai matsala babba kuwa.
“Amma sai muka yi dace Hukumar Tsaro ta Sojojin Sama suka amince za su yi mana jigilar kayan zabe. Dama kuma sun zaba yi wa INEC irin wannan taimakon.” Inji Haruna.
Discussion about this post