A ranar Talata ne babban dan tsohon shugaban kasar Misra, Egypt, Abdullahi Morsi ya bayyana cewa an yi jana’izar mahaifin sa a wani makabarta dake gabas da garin Cairo.
Abdullahi ya ce hukumomin tsaro basu yardan wa iyalan mamacin su rufe shi a makabartar da ake bizine zuri’ar su ba.
Idan ba a manta ba shugaba Mohammed Morsi ya yanke jiki ya fadi ne a zaure Kotu a ci gaba da shari’arsa da ake yi kan tuhumarsa da ake yi na zargin cin amanar kasa.
Morsi wanda dan Kungiyar ‘Yan’uwa musulmai ne da ake kira ‘ Muslim Brotherhood’ ya zama zababben shugaban kasar Masar na farko a shekarar 2012.
Sai dai bai dade a mulki ba sojoji suka yi masa juyin mulki.
Tun daga wancan lokaci yana daure ne bisa zargin wai ya ci amanar kasa inda ya sanar da kasar Qatar wasu bayanan sirri na kasar Masar din.
Gwamnatin kasar Masar ta saka matakan tsaro a wurare da da a domin gudun barkewar hargitsi.