MAJALISAR TARAYYA: PDP ta goyi bayan Sanata Ndume da Hon. Bago

0

A yau Talata ne a Majalisar Tarayya za a yi ta ta kare, wato gwangwa da gwangwa rawar giwaye yayin da a karshe jam’iyyar PDP ta bayyana goyon bayan Sanata Ali Ndume a matsayin dan takarar da za ta goya wa baya a Majalisar Dattawa.

Har ila yau kuma, PDP ta bada sanarwar cewa ta na goyon bayan Hon. Umar Bago a matsayin shugaban Majalisar Tarayya.

Wannan bayani ya na kunshe ne a cikin wata takarda da Sakataren PDP na Kasa, Umar Tsauri ya fitar da jijjifin safiyar yau Talata.

“Bayan mun yi dogon tunani da kuma kwakkwaran nazari tare da tuntubar juna, Kwamitin Zartaswa na Jam’iyyar PDP ya yanke hukuncin goyon bayan Sanata Ali Ndume a matsayin wanda za ta zaba Shugaban Majalisar Dattawa a yau Talata.” Inji Tsauri.

“Mun kuma amince da goyon bayan mu ga Hon. Umar Bago a matsayin Kakakin Majalisar Tarayya. Wannan matsaya an cimma ita tare da dukkanin shugabannin jam’iyya, gwamnonin PDP, Sanatocin PDP da Mambobin Tarayya zababbu a karkashin PDP.”

Sanarwar ta ce wannan shawara da suka yanke ita ce “mafi dacewa ga daukacin kasar nan, domin kara dankon dimokradiyya da kuma gina majalisa mai ‘yancin kan ta ba ‘yar amshin Shata ba.”

Sanarwar ta kara da cewa PDP za ta kara jaddada wa sanatocin ta da kuma ‘yan majalisar tarayya yadda za su jefa kuri’un na su a zaben da za a gudanar yau Talata a Majalisar Tarayya.

LAWAN KO NDUME: Kaka-Tsara-Kasa

Sanata Ahmed Lawan shi Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC ke goyon baya. Haka Hon. Femi Gbajabiamila.
Sai dai kuma wannan bai haka Sanata Ali Ndume kalubalantar Lawan ba. Haka shi ma Hon. Umar Bago ya kalubalanci Gbajabiamila.

Daga a zaben 2015, APC ta ce a zabi Lawan da Gbajabiamila, amma Bukola Saraki da Yakubu Dogara suka nemi goyon bayan wakilan PDP, kuma suka yi nasara.

Daga baya su biyun duk suka koma PDP.

Share.

game da Author