Za a kaddamar da shirin wadata asibitoci da kwararrun malamai (CHIPS) a duk fadin kasar nan – Faisal Shu’aib

0

Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasa (NPHCDA) Faisal Shu’aib ya bayyana cewa gwamnati ta amince a fara gudanar da shirin samar da kwararrun ma’aikata a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin inganta kiwon lafiyar mazauna karkara da ake kira (CHIPS).

Gwamnati ce ta kirkiro da wannan shiri ne domin kawar da matsalolin mace-macen mata da yara kanana a kauyukan da ake fama da su.

Bayanai sun nuna cewa gwamnati ta fara gwada ingancin wannan shiri na (CHIPS) a jihar Nasarawa inda a dalilin nasarorin da aka samu gwamnati ta amince a fara gudanar da shirin a duk fadin kasar nan.

Za a fara shirin ne a sassan kasar nan daga watan Disamba mai zuwa.

Da yake tofa albarkacin bakinsa jami’in Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) Mohammed Fall ya bayyana cewa kaddamar da shirin CHIPS zai taimaka wajen kawar da matsalolin rashin samar da kiwon lafiya mai nagarta ga mutane musamman mazauna karkara.

Fall ya kuma jinjina wa namijin kokarin da Najeriya ta yi wajen ganin ta dakile yaduwar cutar shan-inna a kasar nan.

A karshe jami’ar shirin (CHIPS) Nana Sanda ta ce kaddamar da shirin a jihar Nasarawa ya sa an sami Karin kashi 45 bisa 100 a yawan matan dake zuwa asibiti yin awon ciki sannan shirin ya kuma taimaka wajen karkato da hankulan mata wajen yin amfani da dabarun bada tazaran iyali.

Share.

game da Author