Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar cewa wasu mahara sun kashe mutane 10 a kauyukan Gobirawa da Sabawa a karamar hukumar Safana.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Gambo Isah ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai ranan Laraba.
A wannan takarda Isah ya yi bayanin cewa maharan sun kai wa mutane 150 farmaki a wadannan kauyuka da karfe shida na yammacin Talata.
Ya ce maharan sun far wa kauyukan ne bisa Babura sannan sun saci shannu da dama bayan kashe mutane 10 da suka yi.
Isah yace bayan rundunar ta samu labarin abin dake faruwa ne ta gaggauta aikawa da jami’an ta inda suka yi arangama da maharan.
Ya ce jami’an su sun yi nasaran fatattakan wadannan mahara. Sannan rundunar na iya kokarin ta wajen ganin ta kamo mutanen da suka aikata wannan mummunar aiki domin ganin an hukunta su.
Discussion about this post