Fayemi ya zama Shugaban Gwamnonin Najeriya, Dickon Shugaban Gwamnonin PDP

0

Kwana daya bayan zaben Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi a matsayin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, su kuma gwamnonin PDP sun zabi Gwamnan Jihar Bayelsa, Seriake Dickson a matsayin Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP.

Gwamna Kayode ya gaji mukamin daga hannun Gwamna Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara.

Cikin wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Gwamna Dickon, mai suna Fedilis Soriwaei ya fitar, ya ce tsohon Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP da ya sauka, Ibrahim Dankwambo na Gombe ne ya sanar da haka bayan fitowa daga wani taro da gwamnonin suka yi a Gidan Gwamnatin Gombe da ke Abuja.

Cikin wadanda suka halarci taron har da dukkan gwamnonin PDP, Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Sarkari, na Majlisar Tarayya, Yakubu Dogara, Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus, dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP, Peter Obi da kuma zababben Gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha.

Jim kadan bayan sanar da sabon shugaban kungiyar gwamnonin, Dankwambo ya ci gaba da cewa gwamnonin PDP su na matukar nuna damuwar su da kuma alhinin irin yadda tsaro ke ta kara tabarbarewa a kasar nan.

Gwamnonin sun ce karin abin damuwa shi ne yadda barazanar garkuwa da mutane za ta shafi harkokin noma a cikinn yankunan karkara.

Sun ce abin damuwa ne idan manoma suka ki fita yin noma saboda masu garkuwa da mutane. Wannan cewar su zai haifar da matsala da kuma karancin abinci.

Sun yi kira ga Shugaba Muhammdu Buhari ya sake tashi tsaye ya kara daura damarar shawo kan wannan gagarimar matsala.

Share.

game da Author