Matsalar rashi da tsadar audugar mata ya sa mata ba su iya zuwa makaranta idan al’adar su ta zagayo a Najeriya

0

A bisa sakamakon bincike da ake yi ya nuna cewa ‘yan mata musamman ‘yan shekaru 15 zuwa 19 basu iya zuwa makaranta a duk lokacin da suke jinin al’ada a dalilin rashin kudin siyan audugan da za su saka.

Binciken ya nuna cewa akalla mace daya cikin mata 10 bata iya zuwa makaranta na tsawon kwanaki hudu zuwa biyar duk wata. Wanna ba ga ‘yan mata ya tsaya ba har da matan aure.

Bincike ya nuna cewa mata biliyan 1.2 a duniya na fama da wannan matsalar dake da nasaba da tsananin talauci.

KIRA GA GWAMNATI

Ashley Lori ta yi kira ga gwamnati da ta sa baki a wannan matsala na rashin iya siyan audugan mata da wasu mata da talauci yayi wa katutu suka fama da shi a Najeriya.

Lori ta yi wannan kira ne ta hanyar gudanar da tattaki domin jawo hankalin gwamnati game da wannan matsalar da mata ke fama da shi.

A yanzu haka kudirin kafa dokar maida audugar mata kyauta a Najeriya na nan a gaban majalisar wakilai wanda Lori tace majalisar za ta fara muhawara a kai nan ba da dadewa ba.

Ta ce kamata yayi gwamnati ta rika raba wa mata ‘yan makaranta audugan sannan ta rage farashin audugar a kasuwanni domin sauran mata su iya siya.

” Idan har za a iya raba kwaroro roba kyauta domin samun kariya a lokacin yin jima’I gwamnati za ta iya tallafa wa mata a kasar nan ta hanyar raba musu audugar mata kyauta duk wata.

MAFITA

1. Gwamnati za ta iya rage farashin kudin audugan mata ta hanyar hada kawance da kamfanonin sarrafa audugan domin samar da audugan a farashi mai sauki.

2. Gwamnati za ta iya cire kudin harajin da ake saka wa audugan domin rage tsadar sa a kasuwanni.

3. Gwamnati ta raba wannan auduga wa dalibai mata a makarantu musamman wadanda suke karkara tare da bin diddigi domin tabbatar da cewa ‘yan matan na amfani da audugan yadda ya kamata.

4. Samar da ruwa da gina ingantattun bandaki a makarantu domin mata su iya tsaftace jikinsu.

5. Wayar da kan mata kan yadda za su tsaftace jikinsu a lokacin da suke haila sannan da yadda za su iya zubar da audugan bayan sun kammala amfani da shi.

6. Kafa dokar raba wa mata dalibai audugan mata kyauta.

7. Horas da ‘yan mata kan yadda za su iya dinka audugar da kansu.

Share.

game da Author