Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa mahara sun kashe mutane 23 a kauyukan Tunga da Kabaje dake karamar hukumar Kauran -Namoda.
Jami’in hulda da jama’a Muhammed Shehu ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Talata a garin Gusau.
Shehu ya ce wannan abin tashin hankalin ya faru ne da misalin karfe biyar na safiyar Talata.
Ya ce tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro zaman lafiya ya fara dawowa kauyukan.
A bayanan da ya yi shugaban karamar hukumar Kaura -Namoda Lawal Isa ya ce maharan sun kai sama da 100 a kan Babura da suka far wa wadannan kauyuka a safiyar Talata.
Isa yace suna zaton cewa wadannan maharan sun kawo harin daukan fansa ne a wadannan kauyuka.
” Mun sami labarin cewa wasu ‘yan banga sun kashe wani wanda ke hada baki da maharan mai suna Anas.
” Yan bangan sun gano Anas ne a lokacin da ya dauko matar daya daga cikin maharan domin kaita wajen mijinta a daji.
” Ganin haka kuwa sai wadannan ‘yan banga suka gaggauta tare Anas tare da matan suka kashe su ranar Litini.
Discussion about this post