An yanke wa Ismaila hukuncin bulala 40 saboda shan Mangwaro da gangar da rana ana Azumi

0

A ranar Talata ne kotu a Jigawa ta yanke wa wani saurayi mai suna Ismaila hukuncin shan bulala 40 saboda karya azuminsa da yayi a bainar Jama’a babu gaira babu dalili da rana tsaka.

Alkalin kotun Safiyanu Ya’u ya yanke wa Isma’il wannan hukunci ne bayan hukumar Hisba ta kama Isma’il yana shan mangwaro baro-baro a bainar jama’a bayan kowa na Azumi da gangar.

Ya’u ya ce bisa ga shari’ar musulunci laifi ne babba mutumin dake da cikin koshin lafiya ya ki yin azumin watan Ramadana ba koko ya karya haka kawai ba tare da wani dalili ba da shari’a ya tabbatar.

Ya ce a dalilin haka za a yi wa Isma’il bulala 40 a bainar jama’a domin ya zama ma wasu darasi cewa hakan ba a yi wa addini wasa.

Yace za lallasa bayan Isma;ial a Kasuwa sannan za ayi shela kowa ya fito a taru a gani. Idan aka yi masa haka zai zama darasi ga duk wadanda ke wasa da aikin ibada musamman Azumi.

Share.

game da Author