Daga ranar 29 ga watan Mayu gwamnan jihar Filato Simon Lalong ne zai ci gaba da jagorantan kungiyar gwamnonin Arewa.
Hakan ya biyo bayan taron da kungiyar da ta yi a Kadyna ranar Alhamis.
Gwamnan jihar Barno mai barin gado wanda shine shugaban Kungiyar Kashim Shettima, ya ce gwamnan jihar Filato ne zai ci gaba da jagorantar kungiyar daga inda ya tsaya.
Shettima yace Lalong zai fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Mayu.
A jawabin sa bayan zaban sa gwamna Lalong ya ce lallai zai tabbata yayi aiki tukuru wajen ganin yankin Arewa ta ci gaba matuka. Sannan zai yi koyi da shugaban kungiyar mai barin gado wajen ganin yayi nasara akan wannan gagarimin kujera da ya hau.
” Wannan jagoranci da aka dora min abu ne da ba zan yi wasa da shi ba. Za mu maida hankali wajen ganin yankin Arewa ta samu ci gaban da ya kamata sannan mutanen yankin sun mori ayyuka na ci gaba.