Kungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF), ta kafa Asusun Naira Bilyan 6 domin kaddamar da shirin farfafo da tattalin arzikin yankin.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa mai barin gado, Kashin Shettima ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke bayyana wa manema labarai irin gudummawar da ya samar a shekaru hudu da ya yi ya na rike da kungiyar.
Ya yi wannan jawabi ne ranar Juma’a a Kaduna, yayin da aka kammala taron gwamnonin.
Ya ce an yi wannan hobbasa ne domin yankin Arewa ya samu wani ginshikin dogaro da a kai a fannin inganta tattalin arzki.
Shettima ya ce a karkashin wannan shiri za a farfado da masakar arewa da kuma kamfanin NNDC.
Ya ce jihohin Arwa ne ake sa ran bayar da gudummawar wadannan kudade, tare da cewa ya zuwa yanzu dai an tara naira miliyan 650.
“Domin tabbatar da ganin wannan kyakkyawan kudiri ya tabbata, ana so kowace jihar Arewa daga cikin jihohin 19, kowace ta rika bayar da gudummawar naira miliyan 50 a kowane wata, har tasawon wata shida a jere.
Cikin ababen habbaka arewa da ake son ginawa, har da tashar samar da wutar lantarkimai cikin akalla miga watts 3000 zuwa 4000. Inji Shettima.
Ya ce shirin zai dauki tsawon shekara biyar ana gudanar da shi wurjanjan, wanda kuma za a ga alfanun da zai samar wajen inganta tattalin arzikin Najeriya.
Da ya koma kan maganar matsalar tsaro kuwa, Shettima ya ce a matsayin su na kungiya, gwamnonin Arewa sun kirkiro hanyoyi da matakai da da dama domin dakile matsalar tsaro a kasar nan.
Daga nan ya gode wa Shugaba Muhammadu Buhari bisa gaggawar matakan da ya dauka domin yi wa kufkar zaren matsalar tsaro hanci tun da wuri.