Hukumar EFCC ta kama wani matsafi dake zaune a garin Ilori jihar Kwara, mai sun Jami’u Isiaka.
Shi dai Jami’u ya damfari dan kasar Koriya ta Kudun ne mai suna Keun Sig Kim inda ya rika ce masa wai shine shugaban kamfanin mai na kasa, Maikanti Baru.
A wasu lokuttan ma sai ya ce masa wai shine mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada Labarai.
Jami’u da abokanan damfaran sa sun damfara Kim naira miliyan 30 da sunan wai za su samar hanyar mallakar wani kamfani a Najeriya.
Jami’u wanda matsafi ne ya amsa laifin sa sai dai ya ce ya yi amfani da wadannan kudade ne wajen siyan kayan aiki da nayi amfani da su wajen mallake Kim.
” Kayan aikin da na siya sun hada da Angulu, fatar giwa, hanjin giwa, kwakwalwar zaki, hanjin goggon biri, da wasu kayan aiki.
Nan ba da dadewa ba a gurfanar da wannan matsafi a kotu.
Discussion about this post