A wani bincike da kwararrun malaman asibiti suka yi sakamakon ya nuna irin alfanun dake tattare da yawan shan ruwan dumi ko kuma ruwa wanda ba mai sanyi ba a maimakon sha da amfani da ruwan sanyi a kowani lokaci.
A duk lokacin da yanayi ya canja wato aka shiga yanayi na zafi, zaka ga duk wani abu mai sanyi yana kasuwa matuka.
Babban dalili kuwa shine akan ga shine kawai mafita ga matsanancin kishi da mutum kan ji da rage radadin zafi da aka shawo.
Likitoci da dama da suka zanta da wakiliyar mu sun bayyana cewa ruwan dumi kan warkar da marasa lafiya musamman cutukan da ya shafi ciki.
An gano cewa maimakon samun sauki akan fada cikin matsaloli ne da matsalar kiwon lafiya.
Shan ruwan dumi ko kuma ruwan da bashi da sanyi sosai na da amfani kamar haka:
1. Yin wanka da ruwan dumi na kare mutum daga kamuwa da ciwon sanyin kashi.
2. Yana kare mutum daga kamuwa da cutar hakarkari wato ‘pneumonia’
3. Za a iya samun kariya daga kamuwa da mura.
4. Yana kuma kawar da ciwon ciki.
5. Yana kara karfi a jiki musamman a lokacin zafi da aka fi yawan jin gajiya.
6. Yana taimakawa wajen zurfin tunani.
Discussion about this post