Yadda kuka tikasta a yi wa Buhari Addu’a, ku yi Addu’a a kawo karshe garkuwa da mutane
Malamai sun jajirce sun fito ta kowace hanya sun yi ta kira ga mutane musamman a Arewacin Najeriya da adage da Addu’a shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zarce a zaben 2019.
A wasu lokuttan ma an yi ta maida wannan kira da aka rika yi kamar jihadi za kayi idan har ka dage wajen yi wa shugaba Buhari da jam’iyyar APC Addu’a ka yi.
Allah ya amsa addu’o’in bayinsa bayan bin umarni malamai da mutane suka yi ya maida shugaba Buhari kan karagar mulki.
Tun a wancan lokacin wasu da dama na ganin cewa malamai sun koma yan kwangilan gwamnati ne. Anyi ta yi musu zargin ana basu kudi ne domin suyi amfani da damar da suke da shi wajen ganin mutane sun karkata ga shugaba Buhari da APC dole.
Babban tambaya a nan shine, Anya kakan ‘yan Arewa ta yanke saka da zuwan Buhari kuwa?
Wasu da dama na ganin cewa har yanzu dai anyi nadi ne da lauje a ciki. Mutane na ganin bayan irin bakar wahalar da yankin Arewa ta sha a lokacin mulkin Jonathan game da ayyukan Boko Haram musamman yankin Arewa Maso Gabas, yanzu gaba daya Arewar ce ta shiga cikin halin ha’ula’i.
Tsaro ya zama tashin hankali ga kowa da kowa duk da cewa wannan karon dan Arewa ke mulkin Najeriya, kuma ma Buharin da kowa ya ce shine mai iyawa.
Kasuwanci a Arewa ya na neman ya durkushe a dalillin hare-hare da ayyukan masu garkuwa da mutane.
Babban abin tashin Hankali ma shina abin ya kai ga hatta mahaifar shugaban kasa bata tsira ba daga ayyukan wadannan miyagun mutane.
Masu garkuwa sun far wa garin Daura inda suka yi garkuwa da surikin shugaban kasa kuma Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umaru.
Kaduna, Zamfara, Katsina, Abuja, Sokoto, Nasarawa duk abin babu sauki.
Malamai suji tsoron Allah su fito kamar yadda suka rika fitowa suna cewa sai Buhari, Sai APC su rika gaya wa gwamnati gaskiya sannan a mike tsaye wajen yin Addu’a domin kawo karshen wannan fitina da ya kanannade yankin.