Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, kuma tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya gaskata zargin da Shugaban Riko na Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya yi cewa akwai wasu gwamnonin jihohin kasar nan da ke fakewa da karya ko gaskiyar matsalar tsaro su na sace makudan kudaden jama’a.
Bafarawa wanda ya yi gwamnan jihar Sokoto daga 1999 zuwa 2007, ya jaddada zargin da Magu ya yi a jiya Laraba, dokacin da ya gudanar da taron manema labarai a kan shirye-shiryen gudanar da Taron Makomar Tsaro A Najeriya, wanda Gidauniyar Attahiru Bafarawa Foundation za ta shirya.
Garkuwan na Sokoto ya yi magana da Hausa, wajen amsa tambayar, ya ce tabbas Magu ya yi gaskiya, kuma ya na goyon bayan sa.
“Wato kamata ya yi gwamnonin yanzu su dauki darasi daga gare mu, mu da mu ka yi mulki tun can baya. Su tsaya su dubi yaya wasun mu su ke a yanzu?
“Duk abin da ka tara, to zai kare in dai ba ta hanyar gaskiya ka tara shi ba. Zai kasa gyara firamare da sakandaren da ’ya’yan talakawa ke karatu, amma zai tura na sa ’ya’yan su yi karatu kasashen waje.
“Da ya ke an yi abin duk a bisa hanyar rashin rike amana, sai na su ’ya’yan su fita waje karatu, su je su dawo sun zama ’yan kwaya.
Don haka Bafarawa ya ce gwamnoni a yanzu su rika tafiya sun a waiwayen bayan su, su ga gwamnonin da aka yi a baya yaya suka kare?
“Idan tara dukiya ka ke takara, to dukiyar za ta watse, dama bai tara dukiyar ta hanyar gaskiya ba.
Bafarawa ya ce taron da Gidauniyar Attahiru Bafarawa Foundation za ta shirya bayan azumi a Kaduna, za a tattauna neman mafitar matsalar tsaron da ta dabaibaye kasar nan ce, da nufin samo mafita.
Ya nesanta taron da siyasa, yayin da ya kara da cewa kuskure ne masu adawa su rika murna idan kasa ta shiga mamuyacin halin da kowa ke ji a jikin sa.
“Shi dai mai garkuwa da mutane babu ruwan sa da kai ko dan PDP ne ko dan APC. Kuma ba daidai ba ne kowane laifi a ce shugaba ne yay i.
“Dalili kenan mu ke neman gudummawar kowa, domin a nemo mafita, saboda matsalar ta shafi kowa.
Daga nan ya koka a kan matsalar rashin aikin yi, talauci, rashin ilmi da sauran matsalolin da ake ganin sun haddasa tabarbarewar tsaro, musamman a Arewa.
Duk da haka, Bafarawa ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya kasa cimma wasu nasarori ne, saboda bai samu wadanda za su ba shi maganin da za a sha a warke cutar da ke addabar mu ba.
Sanna kuma ya nuna damuwa yadda kasha-kasha ke ta faruwa a yankunan karkara, inda akasari babu ingantaccen tsaro. Ga kuma yadda rikicin ke haifar da dimbin asarar rayukan matasa da kudiyoyi.
ZARGIN DA MAGU YA YI WA WASU GWAMNONI
Magu ya yi wannan bayani ne a yayin da ya ke jawabi a kan cin hanci da rashawa a wurin taron Sanin Makamar Aikin Zababbun Gwamnoni, a Abuja.
Ya ce yanayin matsalar tsaro da kuma ta’addanci sun kara hauhawar cin hanci da rashawa, ta yadda wasu gwamnonin jihohi ke wawurar kudade salum-alum.
“…Har tulin hujjoji gare mu, wadanda ke tabbatar da yadda wasu gwamnonin jihohi ke kwashe kudade ta hanyar amfani da dalilai na matsalar tsaro.
“Kai a na ma rade-radin cewa wasu gwamnonin kiri-kiri su ke kara rura wutar matsalar tsaro a jihohin su, domin su kara yawan tulin kudaden da suke warewa kan matsalar tsaro.
“Ba sai ma na shiga na yi nisa a batun kwasar kudi da sunan matsalar tsaro ba. abu mafi muhimmanci dai shi ne gwamnoni su yi taka-tsantsan wajen kashe kudaden jama’a. Kuma duk abin da za su yi, su guji harkalla da kumbiya-kumbiya. Su yi komai kan ka’ida kuma a sarari.”
Discussion about this post