Hukumar Kwastan ta nuna takaicin yadda wasu ‘yan damfara suka yi kokarin handame shinkafar da Gwamnatin Tarayya ta ware domin raba wa ‘yan gudun hijira da masu karamin karfin da ba su iya ciyar da kan su.
Kakakin Yada Labaran Kwastan Shiyyar Minna, Jihar Neja, Joseph Attah ne ya yi wannan bayani ga manema labarai.
Attah ya ce gwamnati ta kafa kwamitin raba shinkafar da kwastan suka kama ta sumogal ga sansanonin gudun hijira da gidajen marayu.
Ya bada labarin yadda mutane suka rika kai takardun bogi masu nuna wai su na da gidajen marayun da suke ciyarwa.
“Mun ce kowa ya kawo takardun shaidar ya na da gidajen marayun da ya ke ciyarwa. An kawo mana takardu har 56.
” Amma ya zuwa yau mun tantance 30. A cikin 30 din 6 ne kadai sahihai, sauran 34 duk ‘yan wala-wala ne.
“Akwai ma wani mutum da ya ce mana ya na ciyar da gajiyayyu. Amma da mu ka bi shi domin gani da ido, sai ya kai mu wani masallaci, wai a can ya ke ciyar da mutane.”
Attah ya ce akwai buhunan shinkafa har 12,000 da kuma man girki da za a raba a jihohin Neja, Kwara da Kogi.
Ya ce kwamitin raba kayan agajin ce za ta biya kudin jigilar kai kayan har zuwa wurin wadanda aka baiwa.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da an raba buhu 250 ga wani sansanin gudun hijira a Zungeru, kuma an raba 150 a wani Gidan Marayu na Gwamnatin Tarayya a Minna.