ZAMFARA: Mahara sun kashe shugaban ‘yan bangan da suka dade suna nema ruwa a jallo

0

Mahara dauke da zaratan bundigogi sun kashe shugaban ‘yan banga da suka dade suna farautar sa a garin Rukudawa, dake karamar hukumar Zurmi, jjihar Zamfara.

Shugaban ‘yan bangan mai suna Rabiu Maiwelda ya gamu da ajalin sa ne bayan maharan sun cimma sa a gidan sa a daidai yana yaben katangar gidan.

Kamar yadda wani ganau ya bayyana wa manema labarai, maharan sun shigo garin Rukudawa da rana tsaka ne dauke da bindigogi tsirara suna ta harbi a sama.

Da suka isa gidan sa sai suka nemi ya sakko daga sama inda yake yaben katangar gidan sa. Da ya ki sakkowa sai suka bude masa wuta. Amma abinka da shiryayye, bidigar bata iya huda sa ba.

Daga nan ne suka sakko da shi daga sama da karfin tsiya suka daure shi a bainar jama’a suka rika rotsa masa kai da sauke masa duwatsu a kai har sai da ya mutu.

Mutanen kauyukan Zamfara sun bayyana cewa magaran dake addabar mutanen jihar duk sun dawo cikin gari adalilin bamabamai da ake yi musu lugude a dazukan Zamfara din.

Bayan haka sun bayyana cewa maharan na da masu kai musu bayanan sirri a garuruwan suna masu kira ga gwamnati da su kara kaimi wajen ganin ganin sun bi sahun wadannan mahara domin gamawa da su.

Share.

game da Author