RAHOTON MUSAMMAN:RIKICIN ZAMFARA: Daga Ina Zuwa Ina?

0

Shekaru goma bayan kafa shari’ar Musulunci a Jihar Zamfara, sannan kuma shekaru 13 bayan kirkiro jihar daga Jihar Sokoto, a ranar 1 Ga Oktoba, 1966, Zamfara ta afka cikin mummunan rikicin kashe-kashe, satar dabbobi musamman shanu da kuma garkuwa da mutane.

Daga cikin Kananan Hukumaomi 14 da ke jihar, 8 su na fama da mummunan harfaki da hare-haren ‘yan bindigar da suke neman su garari kowa a Zurmi, Birnin Magaji, Anka, Tsafe, Maru, Bungudu da Maradun. Sauran kananan hukumomin ma ba su tsira ba, sai dai idan ana kukan karaya, to ba a maganar targade.

Mazauna kauyuka irin su Tungar Baushe, Guru, Kizara, Dansadau, Dangulbi, Rukudawa, Gadali, Katuru, Mashema, Birnin Tsaba, Kwabtari, Kungurmi, Ruwan Misa, Dohuwa, Taka Tsalle da kauyuka masu yawa a Kananan Hukumomin Maraduna, Maru, Tsafe, Birnin Magaji, Anka, Bungudu, Shinkafi da Zurmi, sun manta yadda dadin zaman lafiya ko kwanciyar hankali ya ke.

YADDA TARON CIMMA KASHE FITINAR ZAMFARA BAI KASHE FITINAR BA

PREMIUM TIMES HAUSA ta tabbatar da cewa a ranar 15 Ga Disamba, 2016, an gudanar da taron neman cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta hanyar ajiye makamai.

An gudanar da taron a kauyen Gobirawa Chilli da ke kusa da garin Dansadau, cikin Karamar Hukumar Maru.

Cikin manyan jami’an gwamnati da suka halarci taron, har da Mataimakin Gwamna, Ibrahim Wakkala, akwai shugabannin hukumomin tsaro da suka hada da GOC na Rundunar Sojoji ta 1 da ke Kaduna, Kwamandan Sojojin Zamfara, Shugaban SSS na Zamfara, Kwamishinan ‘Yan Sandan Zamfara, Sarakunan Gargajiya da kuma wasu gaggan ’yan bindiga a karkashin Buhari Tsoho, wanda ake kira da lakabin Buharin Daji.

Da farko an fara samun nasarar taron, domin an tabbatar da cewa ‘yan bindiga kimanin 1000 masu kai hare-hare a dazuka Zurni sun ajiye makaman su.

Sai dai kuma yarjejeniyar ba ta yin karko ba, saboda abin da wasu da dama suka kira sakacin gwamnati da kuma matsalar wani bangare na maharan wadanda ba su shiga cikin yarjejeniyar ba.

A wurin taron, an baje matsaloli a faifai, kuma an nemi sulhuntawa.

A na su bangaren, da yawan ‘yan bindigar, wadanda akasarin su Fulani ne, sun jaddada cewa su fa ba barayin shanu ba ne, amma sun tanadi makamai ne saboda an kyale ana satar musu shanu ba tare da jami’an tsaro sun yi wani abu ba.

Sun kuma yi korafin cewa ‘yan sintiri na bin su su na kashewa, ana kwace musu dabbobi, ba tare da yin cikakken binciken gane wane ne dan fashi ba.

Sun sha alwashin ajiye makamai, matsawar aka daukar musu alkawari cewa jami’an tsaro za su kare lafiyar su da ta dabbobin su da ake kwashewa da rana tsaka ko da dare.

ZAMFARA: Asarar Rayuka 3000 Da Gidaje 2000 Daga 2011-2018

A Ranar 25 Ga Agusta, 2018, ne Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara ya bayyana cewa cikin shekaru bakwai, wato daga shekarar 2011 zuwa 2018, an halaka mutane sama da 3,000 tare da banka wa gidaje sama da 2000 wuta a Zamfara.

Abdullahi Shinkafi ya kuma ce akalla Gwamnatin Jihar Zamfara ta kashe sama da naira bilyan 17 a cikinn shekaru bakwai, wajen taimaka wa jami’an tsaro da kudaden alawus, samar musu matsugunai, sayo musu motocin zirga-zirgar yin sintiri da sauran su.

Sakataren ya kuma ce an kona motoci sama da 500 a cikin shekaru bakwai.

Sai dai kuma bai fadi ko adadin shanu nawa ne aka sace a cikin shekaru bakwai a Jihar Zamfara ba.

KASHE BUHARIN DAJI BAI KASHE FITINAR ZAMFARA BA

A Ranar 14 Ga Maris, 2018 ne aka bada sanarwar an kashe Buharin Daji, bayan ya tada tubar da ya yi, inda a cikin 2016 ya ajiye makamai a taron zaman lafiyar da aka gudanar a Gobirawa Chilli.

Wasu mahara ne suka yi masa tawaye, inda suka bude masa wuta. Wannan ya sa ba Jihar Zamfara kadai ba, duk Arewacin Najeriya an yi tsammanin za a samu raguwar fitintinu a jihar Zamfara. Amma abin sai kara muni ya yi.

KOKARIN DA JIHAR ZAMFARA TA YI

Sakataren Gwamnatin Tarayya Abdullahi Shinkafi, ya ce Gwamnatin Zamfara ta kashe kimanin naira bilyan 17 a tsakanin 2011 zuwa 2018 a kokarin kawo karshen rikicin Jihar Zamfara.

Ya ce baya ga bayar da tallafi ga wadanda rikici kan shafa, gwamnati ta taimaka wajen bayar da alawus ga jami’an tsaro, samar musu gidajen zama da kuma sayen motocin sintiri ga jami’an tsaro.

“Mun sai wa jami’an tsaro motoci masu tarin yawa a cikin 2011. A cikin 2014 mun sake sai musu motocin sintiri 77. Daga 2015, 2016, 2017 da 2018 kuma, a kowace shekara mu na sai musu motocin sintiri 50.”

KAMAR DA GASKE: An Lalata Haramtattun Makamai 5,870 A Zamfara

Ranar 15 Ga Mayu, 2018 ne Kwamitin Shugaban Kasa Kan Raba Al’umma da Kananan Makamai a Gusau, ya lalata makamai har guda 5,870 wanda Gwamnatin Jihar Zamfara ta karbe.

An fara gudanar da aikin lalata makaman ne da aka karbe daga hannun wadanda suka mallake su ba kan ka’ida ba.

Akasarin makaman an karbe su ne daga maharan da suka jaddada tuba, kuma suka mika makaman da kan su ga gwamnati a karkashin wani shiri da ke hannun mataimakin gwamnan jihar, Ibrahim Wakkala.

An lalata makaman ne a babban filin balekolin jihar Zamfara da ke Gusau, karkashin sa-idon shugaban kwamitin, Emmauel Imohe.

Cikin wadanda suka halarci taron akwai Gwamna Abdul’aziz Yari, Mataimakinn sa Wakkala da kuma wakilai daga Kungiyar Tarayyar Turai, ECOWAS da UNPD da jami’an tsaro da kuma sarakunan gargajiya.

Shugaban Kwamitin, Emmauel Imohe, ya ce baya ga aikin karbar makaman da lalata su, gwamanati kuma za ta tabbatar da an sake raya yankunan da wannan kashe-kashe ya yi wa illa.

ZAMFARA: Wace Rawar Gani Ministan Tsaro Ya Yi Cikin Shekaru Uku?

Wata Kungiyar Sa Kan Neman ’Yancin Jama’a, mai suna PAIR, ta dora alhakin mummunan kashe-kashen da ake yi a Jihar Zamfara a kan Ministan Tsaro, Mansur Dan Ali, maimakon Gwamna Abdul’aziz Yari.

Ba PAIR ce kadai ta dara wa Minista Dan Ali wannan alhakin ba, har da Kungiyar SGE, NeO da TPC, dukkan su kungiyoyi ne na kwatar wa marasa karfi ’yanci, kuma sun ce Minsitan Tsaro ba shi yin wani gagarimin hobbasan da za a gani har a yaba cewa da gaske ya ke yi wajen ganin an magance fitinar.

Gamayyar Kungiyoyin sun ce Yari ya yiniyakar kokarin da dokar kasa ta wajabta masa, ta hanyar bayar da taimakon kayan aiki, sadarwa da bayanai, bayar da gidaje da kuma alawus na musamman ga ‘yan sanda da sojojin da aka tura a Zamafara, ba tare da wani samun taimako daga Ma’aikatar Tsaro ba.

A cikin wata sanarwa da Isa Yaro ya sa wa hannu, a madadin Gamayyar Kungiyoyin, a jiya Lahadi a Abuja, ya nuna rashin jin dadin yadda Gwamnatin Tarayya ta kasa shawo kan wannan fitina a Jihar Zamfara sama da shekara biyu.

Isa ya ce tun tuni ya kamata a ce Shugaba Muhammadu Buhari ya kori Ministan Tsaro, Mansur Dan Ali.

“Me ya sa za a yi ta dora laifi ga Gwamna Yari, alhali shi gwamna ne kawai, ba shi ke da iko a kan ‘yan sanda da sojoji ba. da dadewa Yari ya sha jan hankalin gwamnatin tarayya game da yadda ake ta jigilar makamai zuwa jihar Zamfara, amma wadanda ya kamata su dakile abin daga tarayya ba su yi komai ba.

“Mu abin da mu ke son sani shi ne, wane irin kokari Ministan Tsaro, wanda dan Jihar Zamfara ne ya yi da za a iya jinjina masa wajen shawo kan kashe-kashe a Jihar Zamfara?

Yaro ya ce ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya yi karatun ta-natsu, ya san irin mutanen da zai nada kan mukamai idan an shiga sabon zangon mulki na biyu a ranar 29 Ga

MATSALAR ZAMFARA: Ta Gagari Gagarau Ne?

A ranar 19 Ga Maris, 2019 ne, Gwamna Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara, ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya yi kururuwa dangane da yadda mahara a jihar sa suke ta kara tanadar makaman da suke ci gaba da kisan jama’a, kona kauyuka tare da yin garkuwa da jama’a.

Yari ya sanar da haka a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, jim kadan bayan ganawar sa da Buhari, inda ya yi masa karin bayanin halin da jihar ke ciki a hanlin yanzu.

Gwamna Yari ya ce ba zai sake shirya wani zaman sasantawa da masu garkuwa da kisan mutane a jihar ba.

“Na shaida wa jama’a ta cewa har na kammala wa’adi na ba zan sake yin zaman sulhu da mahara wadanda suka addabi jihar mu ba. Saboda na yi haka har sau uku a baya, amma zaman sulhun bai tsinana amfanin komai ba.

“Misali, a zaman sulhun da aka yi na farko, sun gayyaci wasu jami’an mu, sojoji, ’yan sanda, DSS da kuma babban jami’in tsaro na. Sannan kuma an gayyaci wakilan sarakunan gargajiya.

“Mun ga irin shirgin muggan makaman da suke da shi, wanda jami’an tsaron jihar Zamfara ba su ma da irin kwatankwacin su.

“A cikin rumbun ajiyar su daya kawai mun ga sama da AK 47 sun fi 500.

“Kai saboda rainin wayo ma har kyale tawagar mu suka yi suka dauki hotunan tulin makaman da suke da su.

“Amma da muka ce to a zauna a yi zaman sulhu, su mika makaman su, mu kuma mu yi musu afuwa, sai suka ki amincewa.

“To ina tabbatar muku da cewa tun daga waccan rana zuwa yau, har yau ba mu karbi AK 47 guda 90 a hannun su ba.

“Saboda tsabar yaudara, a cikin rani sai suka nemi a yi zaman sulhu, saboda sun san cewa jami’an tsaro za su iya cim masu a duk inda suke, tunda babu sauran wuraren da za su buya.

“Amma da damina ta zagayo, ciyayi da tsirrai suka fito, har suka samu wuraren buya, sai suka ci gaba da hare-haren da suke kaiwa.

Yari ya ce idan ba karfin sojoji aka yi amfani da shi ba, to ba za a iya murkushe maharan da suka addabi jihar Zamfara ba.

Ya kara da cewa kwanan nan za a kara loda manyan makamai zuwa Zamfara domin a yi ta ta kare da mahara a jihar.

ZAMFARA: Ko Gwamnati Ta Cika Alkawari Ga Wadanda Kashe-kashen Ya Kassara?

A ranar 25 Ga Agusta, 2018, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Kasar nan, ta bayyana cewa ta na shirye-shiryen gyara wasu gine-gine na gwamnati da maharan da suka addabi jihar Zamfara suka lalata wasu yankunan jihar.

Daraktan Riko na Sashen Yada Labarai na Hedikwatar, John Agim ya ambaci haka a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Burgediya Janar Agim, ya bayyana wa manema labarai a Gusau cewa ayyukan da sojojin za su gudanar sun hada gina rijiyon burtsate, gyaran ajjuwan makarantun da suka lalace da kuma dakunan ganin likita ko na shan magani a yankunan da rikice-rikice suka shafa.

Ya kara da cewa kuma sojojin a su gudanar da ayyukan duba lafiya da bayar da magana a cikin karkarar da mahara suka yi barna.

Ya ce a lokaci guda kuma za a inganta matakan tsaro a cikin yankunan.

Ya jaddada cewa sojojin ‘Operation Sharan Daji’ na ci gaba da gudanar da shirin kakkabe mahara a cikin nasara a duk lokacin da suka nausa gaba ko suka kai farmaki a kan ‘yan ta’addan.

“Mu na samun nasarar kwato dabbobi, muggan makamai da ma wadanda maharan ke yin garkuwa da su.”

ZAMFARA, KATSINA DA BIRNIN GWARI A JIYA DA YAU: ‘Abin Da Ya Ci Doma Ba Ya Barin Awai’

Hare-haren da ake fama a Jihar Zamfara tuni ya fantsama zuwa dajin Birnin Gwari da kuma Jihar Katsina. Tun daga dazukan Birnin Gwari da Katsina da Zamfara, ya kasance wuraren sun zama yankunan da Fulani kan tafi kiwon shanu da rani, sannan idan damina ta yi sai su koma jihohi ko yankunan da suka fito.

Sannu a hankali sai Fulani suka yi kaka-gida a cikin dazukan. Sun su na kafa mashekari, har suka koma gina bukkoki da rugagen samun wurin zama na dindindin.

A hankali dazukan sun yalwanta da jama’a tare da samun karin masu yin kaura daga wasu garuruwan yankin Birnin Gwari da Katsina da Zamfara su na nausawa cikin dazukan.

Batagarin da suka hada da barayi da manyan ‘yan fashi sun rika samun mafaka a cikin dazukan, musamman a yankin dajin Birnin Gwari da Zamfara, inda suka rika fitinar Fulanin cikin daji da sace-sacen shanun su.

Barayi ko ’yan fashin da kan tare motocin ’yan kasuwa masu zuwa Lagos daga Arewa, sun rika komawa cikin dajin Birnin Gwari sun a mazayawa ko nausawa Arewa.

Dalili, saboda shigo da tsarin cire kudi da katin ATM da kuma yin taransifar kudade ta sa ’yan kasuwa sun daina lodar kudade a buhu su na tafiya Lagos ko Anacha da su.

An koma ana amfani da manyan bindigogi ana fashin shanu garke guda, ana lodawa a mota a yi awon gaba da su.

Matsin lamba daga jami’an tsaro ta sa satar shanu ta fara wahala, sai ‘yan bindiga suka maida karfi wajen yin garkuwa da matafiya.

Kaka-gidan da ‘yan fashi suka yi a cikin dajin ya kara janyo da yawa daga barayi na wasu yankuna daban-daban zuwa yin dandazo a dazukan Birnin Gwari da Zamfara suka rika fafarar Fulani da sata, fashi, fyade da kwashe musu shanu.

Da ya ke ‘yan fashin kabilu ne daban-daban, sun rika samun daurin gindin batadarin Fulani wadanda su ba su da yalwar garken shanu da kuma fandararrun cikin su.

Yayin da satar ta yi muni, Fulani sun rika tanadar makamai ganin barnar da mahara wdanda a cikin su akwai Fulani suka rika yi musu.

An kuma wayi gari wasu da aka karkashe wa iyaye ko aka sace musu shanu, idan suka rasa madafa, sai su ma su shiga ayarin ‘yan fashi.

Wata babbar matsala a yanzu ita ce yadda matasa da magidanta majiya karfi ke ta mallakar bindigogin kare kai musamman a Jihar Zamfara.

Shin ta ya gwamnati za ta raba su da bindigogin bayan wannan fitina la lafa ko kuma idan ta zo karshe?

Share.

game da Author