Wani saurayi mai suna Dakar kyma mazaunin jihar Ondo ya babbake ‘yan uwan budurwar sa su 8 saboda ta fasa soyayya da shi.
Shi dai Dakar cikin fushi ya garzaya gidan budurwar sa ne wajen karfe biyun dare inda ya duldula wa gidan fetur sannan ya cinna wa gidan wuta.
Mutane biyar sun mutu nan take sannan uku sun kone amma basu mutu ba. Suna asibiti.
Sai dai kuma ko da Dakar ya far wa wannan gida, ita budurwar tasa mai suna Titi bata kwana a gidan ranar ba.
A halin yanzu dai rundunar ‘Yan sandan jihar na gudanar da bincike akan abin da ya faru bayan tabbatar da aukuwar abin.
Shi dai Dakar ya dade yana soyayya da Titi inda daga baya Titi ta bayyana masa cewa wannan soyayya da suke yi ya isheta haka nan.
Bayan ta fadi wa Dakar, sai gogan naka ya fusata sannan ya aikata wannan mummunar aiki.