NASARAWA: ’Yan takarar gwamna hudu ke kalubalantar nasarar Sule na APC

0

Zaben Gwamna da aka gudanar a watan Maris, 2019, ya wuce, sai dai kuma kamar sauran jihohi da dama, a Jihar Nasarawa ma a kawai sauran rina a kaba.

Bayanai sun tabbatar da cewa ya zuwa yanzu Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta Jihar ta karbi kararraki har guda hudu, inda ‘yan takara ke kalubalantar nasarar da Abdullahi Sule na jam’iyyar APC ya yi a matsayin zababben gwamnan jihar.

Sakataren Kotun Kararraki na Jihar Nasarawa, Bello Sule ne ya furta haka, a lokacin da ya ke magana da manema labarai a jiya Talata a Lafiya, babban birnin jihar.

Muktar ya kara da cewa ‘yan takarar da suka maka Abdullahi Sule kara sun hada da na PDP, PDM, APGA da kuma LP.

Ya yi karin hasken cewa kotun za ta bi kararrakin duk ta bi ba’asin su.

Mukhtar ya ce har yau ba a sa ranar fara sauraren kararrakin ba tukunna, saboda wadanda suka shigar da kararrakin ba su kammala gabatar wa kotu hujjojin su na fara tabka shari’a ba tukunna.

Ya ce akwai adadin kwanaki 180 wadanda za a saurari kara idan an shigar da ita kuma cikin wa’adin kwanakin ne za a yanke hukunci.

Daga nan sai ya ce amma dai ya na da tabbatacin cewa nan da mako mai zuwa za sa ranar fara sauraren kararrakin.

Share.

game da Author