Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa bashin da Najeriya ta ci bai kai yawan da za a ce zai iya fasa mata tulun ciki, ko a ce ya kai iyar wuya ba.
Ta ce kwata-kwata bashin da ake bin Najeriya bai wuce adadin kashi 19 bisa 100 na abin da Najeriya ke samar wa kanta baa batun tattalin arziki ba.
Zainab ta ce a zaman yanzu haka Najeriya ta fi kasashe irin su Ghana, Brazil, Afrika ta Kudu, Masar, Angola da sauran kasashe masu tasowa karfin tattalin arzikin kasa.
‘Yan Najeriya da cibiyoyin hada-hadar kudade da inganta tatalin arziki da kasuwanci na ci gaba da nuna damuwa dangane da dan karen bashin da Najeriya ke ta narka wa cikin ta, da kuma yadda a ko da yaushe bashin ke ta kara hauhawa, tun bayan hawan Gwamnatin Muhammadu Buhari. da daman a ta nuna
Tun da Buhari ya hau mulki cikin 2015, gwamnatin tarayya ke ci gaba da ciwo lamuni ta na gudanar da ayyukan gina kasa wadanda ke cikin kasafin kudi.
Dama kuma babu wadatattun kudaden shiga da za a rika gudanar da ayyukan na kasafin kudi, sai tilas an ciwo bashi.
Jaridu da dama, ciki har da PUNCH sun ruwaito a ranar 15 Ga Maris, 2019, sun ruwaito cewa bashi ya yi wa Najeriya katutu, bayan samun bayanin adadin bashin da aka bin Najeriya, daga Ofishin Kula Da Basussuka Na Najeriya.
Kididdiga daga ofishin na DMO, ta nuna cewa a karkashin mulkin Buhari, daga 2015 zuwa Disamba 2017, an ciwo bashi na naira tiriliyan 9.61.
Hukumar ta DMO ta jaddada a lokacin cewa daga 30 Ga yuni, 2015 ya zuwa Disamba 2017, ana bin Najeriya bashin naira tiriliyan 21.73.
Kididdigar ta nuna kafin Buhari ya hau mulki, ana bin Najeriya bashin naira tiriliyan 12.12 ne ya zuwa 30 Ga Yuni, 2015.
Wato Najeriya a karkashin Buhari ta ciwo bashin naira tiriliyan 9.61 daga Yuli 2015 zuwa Disamba, 2017.
Sai dai kuma duk da yawan wadannan kudade, Ministar Harkokin Kudade ta ce ba wani abin damuwa ba ne, domin tattalin arzikin Najeriya na da karfin da ya sha gaban dimbin bashin da ake bin kasar nesa ba kusa ba.
“Abin dadokar kasa ta ce shi ne kada Najeriya ta ciwo bashin da zai kai kashi 25 bisa 100 na karfin tattalin arzikin ta.
“Mu kuwa bashin da kasar nan ta ciwo bai wuce kashi 19 bisa 100 ba.”
Zainab ta ce Najeriya ba ta shiga sahun kasashe irin su Ghana, Anhola, Masar, Brazil da sauran su, wadanda bashi ya cika musu ciki har sun fara tumbudi ba.