Mahara sun kashe mutum daya sun ji wa mutane da dama rauni a jigawa

0

Wani ma’aikacin karamar hukumar Dutse Muhammad Abdullahi, ya bayyana cewa wasu mahara sun far wa garin Gidan Maidawa dake karamar hukumar Dutse, in da suka kashe mutum daya sannan suka ji wa mutane da dama rauni.

Abdullahi ya ce maharan sun far wa kauyen ne da misalin karfe 2:30 na dare suna harbi ta ko ina.

” Wadanda suka samu rauni suna asibiti ana duba su.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Audu Jinjiri ya tabbatar da aukuwar haka a wannan gari na Gidan Maidawa.

Share.

game da Author