Jiya Laraba da dare a ka yi ta ta kare a tsakanin sauran kungiyoyi hudu da suka rage a Gasar Kofin Zakarun Turai, wato Champions League.
Dama tun a ranar Talata ne Barcelona ta kori Manchester United, ita kuma Ajax ta fatattaki Juventus.
A wasan da aka yi jiya Laraba kuma, Kungiyar Tottenham da ke birnin Landan ta kori Manchester City, ita kuma Liverpool ta kori FC Porto.
MANCHESTER UNITED ta kai ga wannan matakin wasa ne cike da burin ganin cewa za su yi namijin kokari, ganin yadda su ke samun nasara a kwanan nan, tun bayan zuwan sabon dan kociya, Solkjaer.
Sai dai kuma ganin cewa da Barcelona aka hada su, da yawan masu sharhin kwallon kafa sun rika cewa Manchester ta taras da iyakar ta.
Hakan kuwa aka yi, domin a wasan farko, har gida Barcelona ta je ta jefa mata kwallo daya. A wasa na biyu kuma a Barcelona, an jefa wa Manchester United kwallaye uku.
Korar Manchester ya jefa magoya bayan ta a duniya cikin bakin ciki, musamman a tunanin wasu daga cikin su shi ne, kungiyar za ta iya mamaita abin da ta yi wa Barcelona shekaru 20 cif da suka shude, inda Manchester ta je har gida ta caskara Barcelona.
MANCHESTER CITY ta ga samu kuma ta ga rashi, a jiya Laraba da dare. Kungiyar ta yi karo da sokekeniya da bugayyar jefa ruwan kwallaye tsakanin ta da Tottenham. Su biyun sun jefa kwallaye har bakwai a jiya Laraba da dare.
Sai dai duk da kwallaye 4 da Manchester City ta watsa a ragar Tottenham, wannan bai sa ta yi nasara ba, saboda Tottenham ta ci kwallaye 3. Sannan kuma ta jefa wa Manchester City kwallo daya a maokonni biyu da suka gabata a lokacin da ta je musu wasan farko.
Haushi goma da ashirin ga Manchester City. Na farko dai haushin kwamfuta ta haramta kwallon da Raheem Sterling ya jefa a ragar Tottenham, daidai lokacin tashi wasa.
Sai kuma wani karin haushi, shi ne duk da cewa Shugaban Kungiyar Manchester City, Al Monsour ya kashe kusan dalar Amurka milyann 300 wajen sayen sabbin ‘yan wasa, sai ga shi Tottenham ce ta fitar da kungiyar sa.
Tottenham dai a wannan kakar wasan ba ta sayi sabon dan wasa ko na naira dubu biyar ba.
Discussion about this post