KAMEN BABURAN ACABA: Gwamnati za ta sa katafila ta rumurmutse babura 2,500

0

Hukumar Taftace Muhalli ta Jihar Lagos ta bada sanarwar cewa za a sa katafila ta rumurmutse baburan okada har guda 2,500.

Wadannan Babura dai hukumar ta ce ta kama su ne a cikin watanni uku kacal, wato daga Janairu zuwa Maris na 2019.

Kakakin hukumar mai suna Adebayo Taofiq ya bayyana haka a cikin wata takardar sanarwa da ya fitar, inda y ace an kama wadannan dandazon Babura ne yayin da su ke bi kan titinan da aka haramta musu su bi a Lagos.

Cikin 2012 ne dai Gwamnatin Jihar Lagos ta kafa dokar haramta wa masu baburan Okada hawa wasu manyan titinan jihar.

Dokar dai ta umarci masu Babura su rika haya a titinan cikin unguwanni kadai.

Shugaban Hukumar Tsaftace Lagos da Kamen Baburan Acaba, Olayinka Egbeyemi, y ace jama’a na yawann kuka da masu baburan haya, inda su ke zargin su da aikata laifuka daban-daban.

Ya ce akwai kuma korafin yadda ake amfani da Babura ana haddasa cinkoson ababen hawa, yi wa masu tafiya kwace da sauran laifuka.

Ya ce akwai hanyoyi da titina 476 da aka amince masu baburan haya su rika haya a kan su kadai. Don haka ya hore su da su tsaya a kannsu kawai.

Share.

game da Author