An yi garkuwa da manajan banki da ’yan uwan sa biyu a Zamfara

0

Mahara sun yi garkuwa da Manajan Bankin First Bank na Karamar Hukumar Bakura, cikin Jihar Zamfara.

An ruwaito cewa an kama Yusif Dare, wanda shi ne Manajan First Bank na garin Bakura tare da wasu ’yan’uwan sa su biyu.

Wadanda aka yi garkuwar da su dai an same su ne har cikin gida, a unguwar Gada Biyu, cikin Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, aka arce da su, a ranar Asabar.

Dare dai kani ne ga dan takarar gwamnan Zamfara a karkashin APC, Dauda Dare.

Daya daga cikin dangin wanda aka kama din ne ya tabbatar wa manema labarai kama manajan bankin na First Bank a Gusau.

Ya ce wajajen karfe 9 na dare aka dira gidan sa aka tafi da shi da wasu dangin sa biyu.

Kakakin ’Yan Sandan Zamfara, Mohammed Shehu ya tabbatar da faruwa garkuwar, kuma y ace ana nan ana kokain gano inda aka yi garkuwar da shi, domin ceto shi.

Daga nan sai ya roki jama’a cewa duk wanda ya ji wani kishin-kishin, to ya gaggauta sanar da jami’an tsaro.

Idan ba a manta ba, cikin makon jiya ne aka yi garkuwa da wani likita dan kasar Koriya ta Kudu a garin Tsafe, cikin Jihar Zamfara.

Share.

game da Author