Da na mutu a hatsarin helikwafta da mutane da dama sun shiga uku –Osinbajo

0

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa da ya hadu a ajalin sa a lokacin da ya yi hatsarin jirgin helikwafta, to da wadanda aka dora wa nauyin kula da tsaron sa sun shiga cikin tsomomuwa.

Osinbajo ya yi hadarin jirgin helikwafta ne a ranar 2 Ga Fabruary, a Kabba, Jihar Kogi.

Shi da sauran wadanda ke cikin jirgin dai babu wanda ya samu rauni sosai. Domin bayan hatsarin, sun ci gaba da gudanar da ayyukan da su ka je aiwatarwa a garin.

Osinbajo ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi a taron taya Shugaba Muhammadu Buhari da shi Osinbajo din murnar sake lashe zabe, wanda aka shirya a cikin Cocin Fadar Shugaban Kasa, a jiya Lahadi.

“Lokacin da hatsarin ya afku, mun ji tsit, ba mu jin motsin komai. Cikin sakan daya kuma sai tunani ya zo min, a raina na ce, da fa mun mutu, to da tsit din dai za a ji gaba daya, ta mu ta kare kenan. Amma Ubangiji cikin ikon sa, muka tsira ko kwarzane a jiki babu wanda ya yi.

“To kun ga Ubangiji ya ceci jami’an tsaron mu. Ita kan ta Gwamnatin Jihar Kogi da ta shiga tsomomuwa. To mu na kara godiya ga Ubangiji.”

Osinbajo ya ce kafin 2015, idan aka ce masa zai shiga siyasa, har ya karade jihohin kasar nan 36 da Abuja, kuma zai zama Mataimakin Shugaban Kasa, to da zai yi tababa.

“Mata ta ta sha tunatar da ni cewa na fa yi mata alkawarin za mu yi rayuwa ba tare da shiga shirgin kwaramniya ba. Amma kuma kun dai ga inda muka tsinci kan mu a yau.

“Saboda ni dai na san ba ni da wata cancantar samun kai na inda na ke a yanzu, duk nufi ne na Ubangiji kawai.”

Share.

game da Author