Hukumar Zabe ta bayyana cewa zaben gwamnan jihar Sokoto bai kammalu ba, don haka ba za ta bayyana sakamakon zabe ba.
Sokoto ta bi sahun jihohin Adamawa, Taraba, Bauchi, Rivers da Filato inda INEC ta ki bayyana sakamakon zabe.
Babban Jami’I mai bayyana sakamakon zabe, Fatima Mukhtar, ta ce an samu kuri’un da aka soke har 30,082, sannan kuma guda 9887,942 ne aka tantance kafin sahihancin su. Su kuma wadanda aka jefa 1,019,024.
Farfesa Fatima wadda itace Shugabar Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, ta ce Gwamna Tambuwal ya samun kuri’u 489,558, shi kuma dan takarar APC, Aliyu Ahmad ya samu 486,145.
Ratar da ke tsakanin jam’iyyun biyu ita ce kuri’u 3, 413 kacal.
Ta ce a cikin kananan hukumomi 22 an soke kuri’u a rumfuna 137 wadanda suka kai adadin 75,403.
Ta ce tunda doka ta ce idan kuri’un da aka soke sun zarce ratar kuri’in da na daya ya bai wa na biyu, to zabe bai kammalu ba kenan. Sai an shiga zagaye na biyu kenan.