Jami’an tsaro sun damke jami’in tattara sakamakon zabe na Karamar Hukumar Ohaji Egbema, cikin jihar Imo.
A zaman yanzu dai jami’in mai suna Kelechi Ezirim ya na hannu ‘yan sanda.
An kama shi bisa umarnin INEC, haka kuma INEC ta sa an kama Jami’in Kula da Zabe na wannan karamar hukuma mai suna Chris Ogbuadu.
An kama su jim kadan bayan sun gabatar da sakamakon zaben gwamna daga karamar hukumar su, wanda wasu jam’iyyu suka yi korafi da sakamakon da suka gabatar.
Su duka jami’an biyu sun amsa laifin sun gabatar da sakamakon zabe na bogi a inda ba a gudanar da zabe ba.
Ezirim ya ce ya na sane da cewa wasu ‘yan jagaliya sun kwace kayan zabe na wasu rumfuna, amma duk da haka ya amince da sakamakon da aka ba shi daga wadannan yankuna da ba a yi zaben ba.
PREMIUM TIMES ta buga yadda aka hargitsa wurin tattara zabe na jihar Imo. Kuma ta ce bangarorin Gwamna Rochas Okorocha ne da na jam’iyyar PDP.