MAJALISAR ADAMAWA: PDP ta lashe kujeru 13, APC 11

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana sakamakon zaben Jihar Adamawa na Majalisar Dokokin Jihar.

Kakakin Yada Labarai na INEC a Adamawa, Rifkatu Maxwell, a fada a Yola jiya Litinin cewa jam’iyyar APC mai mulki ta lashe kujeru 11, yayin da jam’iyyar adawa, PDP ta lashe har kujeru 13.

Sannan ta kara da cewa jam’iyyar ADC ta samu nasarar lashe kujerar dan majalisar ta jiha guda daya tal.

Jihar Adamawa dai nan a kujerun majalisar dokoki 25, kuma 24 duk APC da PDP ne suka lashe su, sai kujera daya da ADC ta yi nasara a kan ta.

Kujerun da PDP ta yi nasara, sun hada na Demba, Gombi, Guyuk, Uba/Gaya, Hong da Jada/Mbulo.

Sauran sun hada Lamurde, Madagali, Nassarawo/Binyeri, Michika da Numan sai kuma Song da Yola ta Arewa.

Jam’iyyar APC a na ta bangaren kuma ta lashe Fufore/Gurin, FuforeVerre, Ganye, Girei da Leko/Koma.

Sauran wadanda APC ta lashe su ne Maiha, Mubi ta Arewa, Mubi ta Kudu, Shelleng, Toungo da Yola ta Kudu.

Ita kuma jam’iyyar ADC ta lashe kujerar Mayo-Belwa kadai.

Jihar Adamawa dai daga can ne dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, a zaben 2019 da aka gudanar, wato Atiku Abubakar ya fito.

Share.

game da Author