An sace limamin Cocin Katolika a Kaduna

0

An sace John Shekwolo, wanda shi ne Limamin Cocin Darikar Katolika a Ankuwa, cikin Karamar Hukumar Kachia, Jihar Kaduna.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da yin garkuwa da shi, kuma su ne suka sanar da sace Shekwolo din.

Shekwolo dai Babban Rabaran ne, kuma sanarwar ta ce an sace shi jiya Litinin wajen karfe 8 na safe.

Wasu mahara ne suka shiga har cikin gidan sa, suka arce da shi inda har yanzu ba a san inda su ke ba.

Haka sanarwar ta tabbatar, daga Kakakin Yada Labarai na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Yakubu Sabo.

Ya ce an tura tawagar wasu jami’an tsaro, kuma su na ci gaba da neman sa a cikin yankin.

Kafin nan kuma dama sai da Babban Limamin Kirista a Kaduna, Daniel Kyom ya fitar da sanarwa ga manema labarai cewa limanin da aka sace din shi ne mai kula da Cocin Katolika na Waliyiya Theresa da ke Ankwa, kusa da garin Kachia.

Sace mutane tare da yinn garkuwa da su ya yi muni kwarai a jihar Zamfara, Kaduna, Katsina, Sokoto da sauran jihohi da dama a kasar nan.

Tun ana yi wa matsalar kallon wani gagarimin laifi, har ta na neman zama wata hanyar sana’ar samar da kudi cikin sauki ga batagari.

Share.

game da Author