Shugaban Riko na Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa a Najeriya wasu mutane da kamfanoni su 32 kacal, sun sace sama da naira tiriliyan 32 na kasar nan, tsakanin 2011 zuwa 2015.
Magu ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ke jawabin bude Taron Horas da Jami’an Tantance Kwangiloli a Hukumomin Gwamnatin Tarayya.
Hukumar Tantance Kwangiloli ta Kasa ce ta shirya taron a ranar Litinin a Abuja.
Wadanda aka fara gudanar musu da sanin makamar aikin dai su ne kashi na daya da aka fara yi wa a cikin 2019.
Yayin da ya ke gabatar da takardar a madadin Magu, Sakataren EFCC, Ola Olukoyede, ba karamar ta’asar asarar kudade a aka yi wa kasar nan ba.
Ya ce da za a samu kashi daya bisa uku na wadannan kudaden da aka sace, za su iya wadatarwa a gina titina masu tsawon kilomita 500, a gina makarantu 200, a ilmantar da yara 4000 daga firamare zuwa jami’a.
Magu y ace wadannan yara 4000 za a iya kashe wa kowanen su naira milyan 25 daga fara karatun sa zuwa jami’a.
Sannan kuma ya ce duk a cikin kudaden za a iya gina gidaje domin masu karamin karfi, har guda 20,000 a fadin kasar nan.
“Babbar barnar da wadannan mutane ‘yan kalilan suka yi wa kasar nan, ta hana a gina wa al’umma wadannan titina ballantana a yi maganar ilmantar da yaran ko gina dubban gidajen. Ta kuma hana samar musu da ingantaccen tsarin samar da lafiya a kasa da ma sauran ababen more rayuwa.”
Daga nan ya ce rashin kyakkyawar tsarin tantance hakikanin kudaden kwangila ne daya daga cikin hanyoyin da ake wawurar kudade, kuma har yau abin bai nuna alamar kawo karshe ba a cikin hukumomin gwamnati.