Mahara sun kashe jami’an tsaro, sun yi garkuwa da jami’an zabe a Katsina

0

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Katsina ta tabbatar da cewa an kashe jami’in ta daya tare da sace ma’aikatan INEC na wucin-gadi su uku da mahara suka yi a lokacin zaben gwamna da na majalisar tarayya.

‘Yan sanda sun kuma bayyana kashe jami’in ‘Civil Defence’ daya.

Kakakin Yada Labaran Jami’an Tsaron ‘Yan sanda, Gambo Isa, ya fitar da sanarwa sau biyu cewa an kashe Kofur Mannir Usman a kauyen Gobirawa Falale, cikin Karamar Hukumar Danmusa.

Ya kara da cewa mahara sun yi garkuwa da ma’aikatan wucin-gadi uku na hukumar zabe, INEC.

Ya ce Usman ne ke tuka mota a lokacin da mahara suka bude musu wuta.
Ya ce shi kuma jami’in civil defence da aka kashe, an kashe shi ne a kauyen Santar Amadi, cikin Karamar Hukumar Kankara, duk a ranar Asabar.

Ya ce mahara sun dira kauyen ne suka rika harbin kai mai uwa da wabi, har suka samu jami’in tsaron a kirji.

Share.

game da Author