ZABE: Hadarin mota ya ritsa da ‘yan sanda 44 a Abuja

0

Akalla ‘yan sanda 44 suka ji ciwo a wani hadarin mota da ya ritsa da su a kan hanyar Gwagwalada, yankin Abuja, babban birnin Tarayya.

Hadarin ya afku ranar Juma’a da dare.

Cikin wadanda suka ji ciwo akwai Sufeto uku da Saje biyu.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN Ya ruwaito cewa wadanda ba su ji ciwo mai tsanani ba an sallame su.

Amma akwai sauran sha daya da suka ji jiki sosai da har yanzu ke kwance a Babban Asibitin Kwararru na Gwagwalada.

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai Riko, Mohammed Adamu, ya ce Hukumar ’Yan Sanda za ta dauki nauyin kula da wadanda suka ji ciwo, kamar yadda a al’adance hukumar ke yi a ko da yaushe irin haka ya faru.

Ya ce wadanda hadarin ya ritsa da su, su na kan hanyar su ne ta zuwa wuraren da aka tura su domin kula da gudanar da zaben kananan hukumomin Abuja shida da aka gudanar jiya Asabar.

Sufeto Janar Adamu ya ce wasu sun ji ciwo kamar karaya, gocewa, buguwa a kai, yayin da ake ci gaba da binciken su kan ko akwai wasu ciwurwukan da ba a kai ga gani ba.

Share.

game da Author