KADUNA: Ashiru na Jam’iyyar PDP ya fadi warwas a karamar hukumar sa ta Kudan

0

Dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP Isah Ashiru ya fadi warwas a karamar hukumar sa ta Kudan a zaben gwamna da aka yi ranar Asabar.

A sakamakon zaben da aka bayyana a zuwa yanzu, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-rufai kuma dan takaran gwamna na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben karamar hukumar Kudan din inda ya samu kuri’u 28, 624, shi kuma Isha Ashiru ya samu 22, 022.

Baya ga kudan Ashiru ya fadi a kananan hukumomin Makarfi, Jaba sannan yayi nasara a karamar hukumar Kaura.

1. KAURA LG
APC – 8, 342
PDP – 38, 764

Collation Officer: Dr. Lucas Maude
2. MAKARFI LG
APC – 34, 956
PDP – 22, 301

Collation Officer: Tijani Abubakar

3. JABA LG
APC – 6, 298
PDP – 22, 976
Collation Officer: Ajibike Maruf Ajibola

4. KUDAN
APC – 28, 624
PDP – 22, 022

Share.

game da Author