Mahara sun babbake gidaje 27 a jihar Nasarawa

0

Gidaje 27 sun kone kurmus a kauyukan Merte da Nendem dake karamar hukumar Akwanga jihar Nasarawa a dalilin harin da wasu Fulani makiyaya suka yi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Samaila Usman ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labarai a garin Lafia ranan Litini.

Usman ya ce rikicin ya fara ne bayan rasuwar da wata matashiya ta yi a asibitin Akwanga a dalilin fyaden da wani bafillatani ya yi.

” Haka ya sa matasan wadannan kauyuka suka hadu suka kai wa rugan Fulanin hari inda suka kashe mutum daya da dabobbi da dama a rugan.

” Daga nan Fulanin suka kai wa kauyukan Merte da Nendem hari inda suka bankawa gidaje 27 wuta.

Ya ce zaman lafiya ya fara dawo wa kauyukan sannan rundunar na kokarin tattaunawa da magabatan kauyukan da na rugan Filani domin gano bakin zaren rikicin.

Usman ya yi kira ga mutanen yankin da su nisanta kansu daga tada fitina da yi wa doka katsalandan.

Share.

game da Author