Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa Alhamis mai zuwa, wato 28 Ga Maris, za ta sake gudanar da wasu zabukan da ta ce ba su kammalu ba a Jihar Adamawa.
A yau Talata ne ta bayyana haka, jin kadan bayan kotu ta ba INEC iznin ci gaba da maimaita zaben.
Kwamishinan INEC na Jihar Adamawa, Kassim Gaidam ne ya bayyana sanarwar tare da cewa tuni hukumar zaben ta yi kyakkyawan shirin gudanar da zaben nan da kwanaki biyu masu zuwa.
Babbar Kotun Jihar Adamawa ce ta jingine umarnin da ta bayar na farko, wanda ta tsaida sake maimaita zaben.
Jam’iyyar MRD ce ta kai kara a gaban Mai Shari’a Abdul’aziz Waziri, inda shi kuma ya ce kotun sa na da hukurin sauraren karar.
Sai dai kuma a sabon hukuncin da ya zartas a yau Talata, ya ce gobe Laraba, 27 Ga Maris zai saurari wancan korafi da MRD ta gabatar a gaban sa, wanda ta nemi kotun ta soke zaben gwamna da aka gudanar a Jihar Adamawa ranar 9 Ga Maris.
MRD ta yi korafin cewa an cire tambarin jam’iyyar a jerin sunayen jam’iyyun da ke takarar gwamna a jihar Adamawa.
sai dai kuma awowi kadan bayan ambata hakan jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba ta amince da ranar 28 ga watan Maris ba a matsayin ranar maimaita zaben jihar Adamawan ba.
Sakataren Shirye-Shirye na jam’iyyar Ahmad Lawal ya sanar da haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a yau Litini a garin Yola.
” Ba tsoron a maimaita zabe muke yi ba amma rashin ganawa da bangaren mu da hukumar zabe bata yi bane ya sa muka ga an nuna mana wariya da kuma tsayar da ranar Alhamis da ta yi a matsayin ranar maimaita zaben maimakon Asabar wato karshen mako.