Kotu ta yanke wa wani direba hukuncin kisa ta hanyar rataya a jihar Ekiti

0

A yau Talata ne kotu a garin Ado Ekiti jihar Ekiti ta yanke wa wani direba mai suna Ajibola Abednego dake da shekaru 40 hukunci kisa ta hanyar rataya kan kisan wani direba da ya yi mai suna Ojo Ogunsakin.

Lauyan da ya shigar da karar Momoh Kamoru ya bayana cewa Abednego ya kashe Ogunsakin mai shekaru 42 a ranar 10 ga watan Maris 2017 a tashar motar Tosin Aluko dake Ado Ekiti a dalili kaurewa da rikici saboda daukar fasinja.

Kamoru yace bayan Ogunsakin ya dauke wa Abednego fasinjan da yake sa ran samu sai Abednego ya zuciya ya dauki dutse ya harbi Ogunsakin inda hakan ya yi ajalinsa.

Kamoru ya kuma gabatar da shaidu shida da suka tabbatar wa kotun cewa Abednego ya aikata haka amma shi kuwa Abednego ya musanta aikata hakan.

A karshe alkalin kotun Lekan Ogunmoye ya yanke wa Abdenego hukuncin kisa ta hanyan rataya.

Share.

game da Author