Yara 6,000 za su iya kamuwa da cutar Kanjamau daga jikin uwayen su a 2019 a Jihar Kaduna -UNICEF

0

Asusun tallafa wa yara kananan na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna data kara zage damtse wajen ganin ta kare yara kanana daga kamuwa da cutar Kanjamau.

UNICEF ta yi wannan kira ne bisa ga sakamakon binciken da ta samu wanda ke nuna cewa yara 6,000 za su iya kamuwa da kanjamau daga jikin uwayen su a 2019 idan ba a gaggauta daukan mataki ba.

Jami’in UNICEF Zakari Adam ya sanar da haka a taron hada karfi da karfe da matan shugabanin kananan hukumomin jihar Kaduna suka yi domin d gujewa fadawa wannan matsala.

An yi wannan taro ne a ranar Litini a garin Kaduna.

Adam ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta iya kauce wa wannan matsalar ne idan ta karfafa shirin kare jarirai daga kamuwa da kanjamau daga jikin uwayen su, wato (eMTCT).

eMTCT shiri ne da UNICEF ta shigo da shi domin samar wa matan da suka kamu da kanjamau kula sannan da samar da kariya wa yaran da uwayen su ke dauke da cutar.

Ko da yake wannan shiri na da matukar amfani amma wasu matsaloli da suka hada da rashin ware isassun kudade, rashin isassun magungunan kanjamau da kayan gwajin cutar, rashin kwararrun ma’aikata, rashin ganin mahimmancin zuwa asibiti yin awon ciki da haihuwa a asibiti da wasu mata ke kin yi na kokarin yi wa shirin kafar angulu.

” A dalilin haka ne UNICEF ta shirya wannan taro domin samun goyan bayan matan shugabanin kananan hukumomi don samun nasarar kare kiwon lafiyar mata da yara kanana kafin nan da 2020.

Bayan haka kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kaduna Paul Dogo ya yaba da wannan taro da UNICEF ta shirya inda ya kara da cewa gwamnatin jihar ta taka rawar gani wajen ganin an dakile yaduwar jutar ga musamman mata da jarirai.

” Yaduwar cutar Kanjamau a jihar Kaduna ya ragu daga kashi 11.6 a 1999 zuwa 1.1 a 2018. Sannan gwamnati ta yi kokarin gina asibitocin da ke kula da masu fama da wannan cuta da kuma samar da magunguna da kayan gwaji a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko dake jihar.

” A yanzu haka dai muna bukata kara wayar da kan mata musamman mazauna karkara game da mahimmancin kare kansu da ‘ya’yan su daga kamuwa da cutar sannan da inda za su iya samun kula ko da sun kamu da cutar.

A karshe a madadin matan shugabanin kananan hukumomin jihar, matar shugaban karamar hukumar Zariya Amina Bamalli ta ce matan za su ci gaba da mara wa wannan shiri baya 100 bisa 100.

Share.

game da Author