Wani abu da ya yi kaurin suna yanzu musamman ga mata shine yadda mata ke yawo babu kamfai a jikinsu.
Mata sun gwamace su rika yawo babu kamfai a jikin su saboda gudun cin karo da matsafa wanda ake kira da ‘Yahoo boys’ dake bin mata suna kwace musu kamfai da karfi da tsiya.
Da farko wadannan matasan sun fara da sace kamfen mata ne idan aka shanya su a waje sai dai a hankali wannan abu nasu sai ya dauki wani salo da yanzu matasan na kwace kamfen ne da karfin tsiya. Sai su ko nuna musu bindiga ko makami su ce ta cire ta basu ko su illata ta.
A wa su lokuttan ma ko da bak saka ba sai su ciro daga aljihun su su mika miki suce sai kin saka da karfin tsiya sannan ki cire bayan wasu ‘yan mintuna ki mika musu su yi tafiyar su.
Kafafen yada labarai su ruwaito sau da dama yadda irin wadannan matsafa ke bin gida gida suna sace kamfen mata.
Wasu masanan wannan harka sun bayyana cewa matsafan na amfani da kamfen matan ne idan suka kwace domin yin asirin neman sa’a a sana’ar damfara da suka yi.
Ba kamfai ba kadai wadannan matasan ma na hadawa da audugan al’ada ds mata suka yi amfani da.
An ce daga baya irin wadanda aka kwace wa kamfai, sukan burkice, wasu su lalace wasu ma har mutuwa su kan yi.
Illar wannan mummunar abu ga macen da aka karbe wa kamfan ta shine haukacewa,rasa saun sa’a a duniya wata sa’a ma har mutuwa matan na yi.
Hanyoyin da mata suka dauka don kauce wa fadawa hannun irin wadannan muggan mutane.
1. Rashin siyan kamfai kwata-kwata.
2. Daina shanya kamfai a waje.
3. Kona kamfai da audugan al’ada da aka yi amfani da su.
4. Kin zuwa gidan saurayi sanye da kamfai.
5. Kin karban kyautan kamfai daga saurayi ko wani.