Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto ta bada hakuri ga PREMIUM TIMES bayan da wasu jami’an ta suka ci zarafin wakilin jaridar, mai suna Taiwo-Hassan Adebayo a Sokoto.
Sokoto na daya daga cikin jihohin da ake maimaita zaben gwamna a cikin su a yau Asabar, wadanda INEC ta ce zabukan da aka gudanar makonni biyu da suka gabata a jihohin ba su kammalu ba.
Adebayo na daya daga cikin ‘yan jaridar da aka tantance su sa-idon dauko labarai a jihar Sokoto.
An ci zarafin na sa ne jim kadan bayan da ya fara aikin tattara labarai a Mazabar Magajin Gari, wadda ke Shiyyar Sokoto ta Arewa.
Wani jami’in dan sanda ne ya hana Hassan kokarin matsawa wata rumfar zabe wajen karfe 9:30 na safe.
“Na shaida masa ni ba mai zabe ba ne, na nuna masa katin tantancewa aikin zane nawa, a matsayi na na dan jarida, sai ya cukume ni, kuma ya fasa min waya ta.”
Hassan ya gargadi dan sandan da cewa ya shiga taitayin sa, kada ya hana shi yin aikin sa na jarida.
Dan sandan ya sake fusata, ya kirawo wasu abokan aikin sa, suka rika musguna wa Hassan.
An kira wani dan sanda mai rike da bulala wai ya bugi Hassan, amma jama’a suka shiga tsakani, aka sasanta.
Kakakin ‘Yan sandan Jihar Sokoto, Sadiq Muhammad ya kira Hassan ya ba shi hakuri, sannan kuma ya yi masa alkawarin za a bincika domin a hukunta jami’an da suka ci masa mutunci.
Ya ce wannan rashin iya aiki da ‘yan sandan suka yi, ba abu ne da za a bar shi haka kawai ya wuce ba, tilas za a hukunta su.