Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta kai ziyara ga wadanda suka tsira daga ibtila’in ruftwar bene a Legas.
Ta kai musu ziyarar ce jiya Asabar bayan da aka tono su daga cikin ruguzajjen benen a unguwar Ita-Faji.
A Asibitin Legas Islanda ta kai musu ziyara, inda suke jiyya kuma ake ba su kulawar da ta dace.
Aisha ta nuna alhinin ta ga wadanda suka rasa rayukan ku da kuma ta’aziyya da jimamin raunukan da wadanda suka tsira da rayukan su ka ji.
Ginin dai ya rufa ne da yara ‘yan makaranta da kuma wasu mutane, inda aka yi asarar rayuka 20.
Aisha ta ziyarci bangaren mata da kananan yara na asibitin, ta yi musu addu’a tare da bai wa iyalan mamata hakurin rashin da aka yi.
Wata malamar makarantar mai suna Easter Samuel, mai shekaru 19, ta bayyana wa Aisha irin gigitar da ta same su.
Ta kuma yi addu’ar kada Allah ya sake kawo irin wannan bala’i.
Rahotanni dai sun ce benen mai hawa uku, dama tun kafin al’amarin an zana masa jan fenti har sau biyu cewa za a ruguje shi, amma ba kai ga yin haka ba.