Tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel ya bayyana cewa ya hakura da jam’iyyar PDP ne saboda isar sa da ita kanta siyasar ta yi.
Daniel wanda shine darektan Kamfen din Atiku ya bayyana cewa ya gaji da siyasar haka ne yasa zai koma ya huta.
Sai dai kuma bayyana hakan ke da wuya sai ya magoya bayan sa a Abeokuta suka roke sa da maimakon ya fice haka nan kawai ya ya jasu duka su koma APC tare.
Idan ba a manta ba tsohon gwamna Gbenga Daniel sai da yayi shekaru takwas ya na gwamnan jihar Ogun a jam’iyyar PDP.
A zaben 2019, shine ya rike mukamin babban darektan kamfen din Atiku Abubakar, dan takakaran shugaban kasa na jam’iyyar PDP.