Ko a gasar shekarar da ta gabata, sai da Manchester City ta kai wasan zagaye na uku. Na san kuma a wannan karon za ta tabbatar da cewa ta yi iyakar iyawar ta domin ganin Tottenham ba ta hana ta kaiwa ga wasan kusa da na karshe ba.
Dama kuma ’yar uwar ta Liverpool da suke kasa daya ce, kamar Tottenham din, ta hana City kaiwa ga wasan kusa da na karshe a gasar 2018.
Tottenham a na ta bangaren ta na ta kumajin ganin ta sabule wa Manchester City wando a tsakiyar sabon filin ta da za ta fara buga wasa a ciki a ranar haduwar ta da City din.
Tottenham su ke janyo wa kan su matsala idan matsin lamba ya yi musu tsanani, kamar yadda shi kan sa kociyan su, Mauricio Pochettino ya taba amincewa da haka.
Sai dai kuma a ranar haduwar su da Manchester City za su so ganin cewa sun guje wa daukar buhun kunya daga filin wasa zuwa gida.
Tabbas za su so tsere wa Manchester City, ko da kuwa da hula da takalma a hannu ne.
A na su bangaren, kociyan City, Pep Gordiola shi kadai ne kociyan da ya rage a cikin gasar wanda a baya ya taba lashe kofin daga kulob takwas da suka rage. Sauran duk ba su taba dauka ba. Ya na cikin matsin-lambar ganin ya ci kofin Champions League a Manchester City.
Sai dai kuma idan ma ya yi nasara a kan Tottenham, to akwai sauran maza a gaban sa, wadanda a baya sun sha zabga wa City dukan tsiya ta na kasa ramawa.
Discussion about this post