ZABE: INEC ta yi kururuwar yawan tashin gobara a ofisoshin ta

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta yi kururuwar nuna damuwa da yawan tashin gobara a wasu ofisoshin ta.

PREMIUM TIMES ta bada rahoton yadda gobara lashe wani ofishin INEC da ke Karamar Hukumar Isiala Ngwa ta Kudu a cikin Jihar Abia, sannan kuma jiya Lahadi ta ruwaito tashin wata gobara a ofishin ta da ke cikin Karamar Hukumar Qua’an Pam da ke cikin Jihar Filato.

Wani mai gadin ofishin Hukumar Zabe da ke Karamar Hukumar Qua’an Pam a Jihar Filato, ya banka wa ofishin wuta, har dukkan kayan zaben da ke ciki gaba daya suka kone kurmus.

Babban Jami’in Wayar da Kai na INEC a Jihar Filato, Osaretin Imajiyereobo, ya tabbatar da cewa wani mai gadin ofishin ne ya banka masa wuta bayan ya yi mankas da giya.

Daga cikin kayan da suka kone kurmus, akwai dukkan akwatunan zaben da za a yi amfani da su, tulin katin rajista na dindindin da masu su ba su kai ga karba ba, rajistar da ke dauke da sunayen masu zabe na karamar hukumar da ke kan takarda da kuma na cikin kwamfuta.

Jami’in ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa zuwa lokacin da ta ke hada wannan labarin, ba a tantance wane mai gadin ba ne.

Wannan gobara ta maida wa aikin INEC hannun agogo baya, a sha’anin gudanar da zabe a Karamar Hukumar Qua’an Pam.

Wannan karamar hukuma ta na daya daga cikin kananan hukumomi shida da suka kunshi shiyyar sanatan Filato ta Kudu.

A kan haka ne Daraktan Wayar da Kan Jama’a da Yada Labarai na INEC, Festus Okoye y ace sun mika koke da wannan kururuwar nuna damuwa ga hukumar ‘yan sanda. Sun nuna damuwar ce sosai ganin yadda ofisoshin biyu ba su tashi konewa ba, sai kwanaki kadan kafin gudanar da zabe.

INEC ta ce duk da haka ba za ta bayar da kai borin wasu masu fitinar banka wa ofisoshin ta wuya ta yi tasiri a kan hukumar ba.

Ta ce babban muradin masu banka wutar shi ne su kawo wa zaben 2019 cikas, kuma ba za su yi nasara ba.

INEC ta dauki matakai hudu domin tabbatar da cewa an gudanar da zabuka a kananan hukumomin da abin ya shafa. Matakan sun hada da:

Umartar Kwamishinonin Zaben Jihar Filato da na Abia su gagganuta sake tattara sunayen wadanda aka kone katin rajistar su da ke ofishin INEC, yadda INEC din za ta gaggauta samar musu wani, kuma su karbi abin su kafin ranar zabe.

Sannan kuma a gaggauta sake zuba sunayen wadanda suka yi rajista a kananan hukumomin a cikin kwamfuta da kuma adana sunayen na su a cikin rajista.

INEC ta ce za ta gaggauta sake aikawa da sabbin kayan zaben duk da aka kona a ofisoshin Kananan Hukumomin biyu da ke Abia da Filato.

Sannan kuma ta umarci da a gaggauta sake wa ofisoshin wani sabon ofis nesa da ofisoshin da aka kone din.

Share.

game da Author