Jam’iyyar PDP ta yi kira ga jami’an tsaro na SSS da ta gaggauta sakin Darektan yada labaran jam’iyyar Ben Bako da ta waske da shi ranar Asabar da yamma a garin Kaduna.
Jigo a jam’iyyar Danjuma Sarki ya sanar da haka ranar Lahadi da yake zantawa da manema Labarai a garin Kaduna inda ya kara da cewa jam’iyyar baza ta zubar da girmanta ba wajen tada rikici a lokacin zabe ba.
Sai dai har yanzu hukumar SSS bata fadi dalilin kama Ben Bako ba sai dai hakan na da nasaba be da Kira da yayi a wajen Kamfen a Kaduna cewa magoya bayansu su lakadawa duk wanda bai zabi jam’iyyar PDP ba dukan tsiya a Kaduna ranar Zabe.
Sarki ya Kara da cewa Jam’iyyar PDP ba Jam’iyyar tada husuma ba ce. Sannan ba zata yi abinda zai sa a yi tashin hankali a lokacin zabe ba.
Bayan haka ya yi kira da a canja shugaban hukumar SSS na jihar Kaduna Ahmadu Idris, cewa yana nuna son kai matuka a aikin sa.
A karshe ya kuma yi kira ga duk masu sa ido a zabe na ciki da wajen kasar nan da su sa ido sosai a aiyukkan zaben da zai gudana a jihar.
Sannan ya yi kira ga mutanen jihar Kaduna da su fito kwansu da kwarkwata su zabi Jam’iyyar PDP.