Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta jaddada cewa za a hukunta dukkan wani wanda ya karya dokokin zabe a bisa abin da tsarin dokar kasa ya shimfida, ba kamar yadda Shugaba Buhari ya fadi ba cewa a harbe wanda ya arce da akwatin zabe ba.
Shugaban INEC ne Mahmood Yakubu ya tabbatar da haka, a lokacin da ya ke yin raddi kan furucin da Shugaba Buhari ya yi a ranar Litinin da ta gabata cewa duk wanda ya saci akwatin zabe a ranar Asabar mai zuwa, za a dirka masa bindiga.
Buhari ya ce an gaji da yadda ‘yan takifen batagari ke dama lissafin zabe a kasar nan. Saboda haka ya bai wa sojoji da ‘yan sanda umarnin duk wanda ya saci akwatin zabe ya nemi arcewa da shi, to a gaggauta dirka mai bindiga kawai.
Shugaban ya ce daga wannan zaben duk wanda ya saci akwatin zabe, to ba zai sake satar akwatin ba har abada.
Tun bayan da Buhari ya yi wannan kakkausa furuce ne ya ke ta shan caccaka daga kungiyoyin kare hakkin jama’a da ‘yan adawa.
Dokar Najeriya dai ta Sashe na 128 ta tanadi hukuncin daurin watanni 24 ga duk wanda aka kama da laifin satar akwatin zabe.
Sannan kuma akwai dokar da ta tanadi daurin shekara da tara ko kuma tara kadai ga wanda ya haifar da rikici a wurin zabe, ko kuma tarar naira 500,000.00.