Za a fara amfani da na’urar rage yawan gudu a motocin mutane – FRSC

0

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta amince wa masu motocin kansu yin amfani da na’uran rage yawan gudu a motocin su.

Jami’in hukumar na reshen jihar Ondo Philip Ozonnandi ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Talata a Ore.

Ozonnandi ya bayyana cewa hukumar FRSC ta kirkiro da wannan doka ne tun shekarar 2016 sannan dokar ta fara aiki ne ranar daya ga watan Faburairu 2017.

” A dalilin haka manayan motoci kamar su tireloli da motocin kasuwa dake Ore ne suka fara amfani da wannan na’ura bayan dokar ta fara aiki.

Ozonnandi ya ce bana hukumar na kokarin ganin mutane masu motocin kansu sun fara amfani da wannan na’ura a motocin kan su.

Share.

game da Author