Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) akalla mutane miliyan 2 da rabi ne suka yanki rajistar kada kuri’a a zaben 2019 da za a fara gudanarwa cikin watan Fabrairu mai zuwa a Jihar Filato.
Kwamishinan INEC mai kula da jihohin Filato, Nija, Kaduna da FCT, Antonia Simbine, ce ta bayyana haka a wani taron wayar da kai a jiya Talata a Jos.
Ta ce daga cikin adadin akwai kashi 50.6 wadanda mata ne, sai kuma 47.3 maza ne.
Ta kuma yi kira ga wadanda suka yi rajista amma ba su kai ga karbar katin rajistar ba da su hanzarta zuwa su karba.
Sannan kuma ta kara nanata cewa INEC ta kammala duk wasu shirye-shiryen da suka wajaba a ce an yi, domin a tabbatar da an gudanar da zabe sahihi mai inganci, adalci kuma karbabbe a cikin kasa da ma duniya baki daya.
Discussion about this post